Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump

[ad_1]



Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa na shirin ɗaukar matakan soja da ka iya haɗawa da hare-haren ƙasa da na sama a Nijeriya.

Trump ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai, inda yake amsa tambayar yanayin yadda hare-haren za su kasance ta sama ko ta ƙasa.

A cewarsa, “komai na iya faruwa, abubuwa da dama za su faru. Ina nufin abubuwa masu yawa,” in ji shi kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.

Shugaban ya ƙara da cewa, “Suna kashe Kiristoci, kuma suna kashe su da yawa. Ba za mu bari hakan ta ci gaba da faruwa ba.”

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Asabar, Trump ya bayyana cewa ya umarci Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon da ta tsara yiwuwar kai hari kan Najeriya.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan ya yi gargaɗin cewa Kiristoci na fuskantar kisan kiyashi a ƙasar.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce tana kallon wannan batu a matsayin lamarin da za a iya warwarewa ta hanyar diflomasiyya, tana mai cewa ƙasashen biyu abokan hulɗa ne wajen yaƙi da ta’addanci.

Cikin wani saƙo da mai magana da yawun fadar gwamnatin Nijeriya Daniel Bwala ya wallafa ranar Lahadi, ya ce idan shugabannin ƙasashen biyu suka gana, akwai fatan samun mafita mai kyau.

Barazanar Trump

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social da tsakiyar daren ranar Asabar, Donald Trump ya ce Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan take idan har gwamnati ta ci gaba da nuna halin ko in kula kan kisan da ake yi wa mabiya addinin Kirista a kasar.

Hakazalika, Trump ya ce Amurka na iya kutsa wa Nijeriya da ƙarfin soji domin kakkabe ’yan ta’adda masu aikata ta’asa da sunan addinin Islama, sannan ya umurci Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka da ta shirya domin yiwuwar kai wa Nijeriya samame.

Wannan furici na Trump na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatinsa ta saka Najeriya a cikin jerin ƙasashen da take da damuwa da su, bisa zargin yi wa Kirista kisan ƙare dangi, lamarin da fadar mulki ta Abuja ta musanta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *