Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
[ad_1]
Sabon ministan harkokin waje na kasar Malawi George Chaponda, ya bayyana cewa, ci gaban tattalin arziki cikin sauri da kasar Sin ta samu na tsawon shekaru da dama ya samar da darussa masu mahimmanci ga Malawi da sauran kasashe masu tasowa ta fuskar ci gabansu.
Chaponda ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba a Lilongwe, babban birnin Malawi, yayin bikin cika shekaru 76 da kafa Jamhuriyar Jama’ar Sin.
Chaponda ya kara da cewa, “Za mu iya koyo cewa mu ma za mu iya samun ci gaba kuma mu amfana ta hanyar yin aiki tukuru, da jajircewa, da mai da hankali sosai, da kin amincewa da cin hanci da rashawa.”
Yana mai cewa, “Malawi za ta iya fita daga kangin talauci ta hanyar karfafa bangaren noma, kuma gwamnatin kasar Sin ta nuna yiwuwar hakan ta hanyar kafa cibiyar noma a Lilongwe, inda manoman yankin ke koyon fasahohin zamani daban-daban.”
Ya yi nuni da cewa, kasar Sin na ci gaba da zama babbar mai taimaka wa ci gaban duniya, musamman ta hanyar shirye-shirye daban-daban kamar Shirin Ziri Daya da Hanya Daya da kuma Dandalin Hadin Gwiwar Sin da Afirka.
A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link