Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?
[ad_1]
Ba za a samu ci gaban tattalin arziki mai dorewa ba, matukar ba a inganta bangaren masana’antu ba. Wannan tamkar ra’ayi na bai daya ne na kasashen Afirka. Sai dai, bangaren masana’antu na kasashen Afirka na ta fama da tafiyar hawainiya, bisa wani tsarin tattalin arzikin duniya da kasashen yamma suke jagoranta. To, amma ina dalilin da ya sa haka?
A ganin Raul Prebisch, masanin ilimin tattalin arziki dan kasar Argentina, dalilin shi ne, kasashen yamma dake jagorantar tsare-tsaren tattalin arzikin duniya sun zama masu fada-a-ji kan sana’o’in da kasashe masu tasowa ke iya gudanarwa, matakin da ya kayyade kasashen Afirka su zama masu samar da danyun kayayyaki wadanda ba a sarrafa su sosai ba.
Duk da haka, wannan yanayi na samun sauyawa, bisa “juyin juya hali” da kasar Sin ta haifar.
A kwanakin nan, jam’iyya mai mulki a kasar Sin, wato jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ta gudanar da wani taron manyan shugabanninta, inda aka gabatar da shawarwari kan matakan da za a dauka wajen raya kasar Sin cikin shekaru 5 masu zuwa. Cikinsu kuma an jaddada bukatar raba karin damammakin samun ci gaba tare da sauran kasashe. To, ta yin la’akari da matakan da kasar Sin ta dauka a baya, da burikan da ta sanya a gaba, a zahiri ne kasar ta mai da samun ci gaba na bai daya tare da sauran kasashe, ciki har da kasashen Afirka, a matsayin wata babbar manufarta da za ta nace a kai cikin dogon lokaci.
To, ko me ya sa kasar Sin ke son ganin ci gaban kasashen Afirka? Saboda kasar Sin tana bukatar samun ci gaban tattalin arziki ita ma kanta. Idan an bari kasashen yamma su ci gaba da tafiyar da tsare-tsaren tattalin arzikin duniya, to, kasar Sin ba za ta taba samun damar raya masana’antu masu kunshe da sabbin fasahohi masu inganci, da zama kasa mai ci gaban tattalin arziki sosai ba, dai dai kamar yadda kasashen Afirka ke fama da matsalar karancin damammakin raya masana’antu. Saboda haka, kasar Sin ta kan jaddada cewa, samun ci gaba wani hakki ne na asali, kuma ya kamata a ba dukkan kasashe, maimakon mai da shi damar musamman da kalilan kasashe ke samu.
Sa’an nan matakin da kasar Sin ke dauka yanzu, shi ne jagorantar manyan gyare-gyare kan tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya, ta yadda ita da dukkan kasashe masu tasowa za su samu damar inganta tsare-tsarensu na tattalin arziki, musamman ma a bangaren masana’antu. Dangane da batun, babbar darektar hukumar kasuwanci ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana a wajen taron dandalin tattaunawa na Abuja karo na 6, da ya gudana a kwanakin baya, cewa “Sauyawar tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya ta haifar da damammaki ga kasashen Afirka, ta fuskar janyo jari, da karfafa bangaren masana’antu.” Ban da haka, ta ce, “Huldar abota tsakanin Afirka da Sin wani misali ne na samun ci gaban da zai amfani kowa ta hanyar hadin gwiwa, ga kasashe masu tasowa”, kana “ Kasar Sin ta iya jagorantar hadin gwiwar, ta hanyar zuba jari ga kasashen Afirka, da taimakonsu wajen raya tattalin arziki.”
Hakika, ma iya cewa maganar Madam Ngozi ta riga ta zama gaskiya, ta yin la’akari da yadda kasar Sin take zuba jari da raya masana’antu a kasashen Afirka daban daban. Sai dai ci gaban masana’antun kasashen Afirka da Sin suna haifar da sauyawar yanayi kan tsohon tsarin tattalin arzikin duniya. Hakan ya sa kafofin yada labarai na kasashen yamma suka dinga yada jita-jita game da kasar Sin, da hadin gwiwarta da kasashen Afirka. To, abun da ya kamata kasashen Afirka da kasar Sin su yi, shi ne rufe kunnuwansu, da kokarin neman ci gaban tattalin arziki, da gina wata duniya mai adalci da samun daidaito. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link