Majalisar Yobe ta nemi a dauki mataki kan yawaitar hadura a hanyar Damaturu–Potiskum
[ad_1]
Majalisar dokokin jihar Yobe, ta yi kira ga bangaren zartarwa na gwamnatin jihar da ta dauki matakan gaggawa domin magance yawaitar haduran ababen hawa a garuruwan Ngelzarma, Damagum da Dogon Kuka da ke kan hanyar Damaturu zuwa Potiskum.
Majalisar ta yi wannan kiran ne bayan gabatar da kudiri da dan majalisa mai wakiltar mazabar Damagum, Maina Digma Gana, ya yi kan yawaitar hadura a wadannan garuruwa.
Gana, ya bayyana cewa yawaitar haduran ababen hawa a yankin abun damuwa ne, don haka ya zama wajibi gwamnati ta dauki mataki don kare rayukan jama’a.
Ya kara da cewa daga watan Janairun 2025 zuwa yanzu, sama da mutane 30 ne suka rasa rayukansu a garin Damagum sakamakon haduran ababen hawa a hanyar Damaturu zuwa Potiskum.
Dan majalisar, ya bukaci gwamnatin jihar da ta gina shatale-tale a Damagum tare da samar da wasu matakan rage gudun mota a titunan da suka ratsa garuruwan Ngelzarma da Dogon Kuka.
Ya ce hakan zai taimaka wajen rage gudu da direbobi ke yi, wanda shi ne ke janyo yawan hadura da asarar rayuka.
Da yake goyon bayan kudirin, shugaban masu rinjaye na majalisar, Nasiru Hassan Yusuf, wanda ke wakiltar mazabar Damaturu, tare da dan majalisa mai wakiltar mazabar Karasuwa, Adamu Dala Dogo, sun bukaci hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) da hukumar YOROTA su kara wayar da kan direbobi kan illar tuƙin ganganci da gudun wuce kima.
Kakakin majalisar , Rt. Honarabul Chiroma Buba Mashio, ya yi kira ga ’yan majalisar da ke wakiltar al’umma a majalisun tarayya da su gabatar da lamarin a gaban majalisar dokokin kasa, domin samun guiwar gwamnatin tarayya wajen magance matsalar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link