An kama mata da miji suna safarar makamai a Kaduna
[ad_1]
Sojoji sun kama wata mata da mijinta da suka yi kaurin suna wajen safarar makamai a yankin Saminaka da ke Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna.
Dubun ma’auratan ta cika ne a wani shingen binciken inda sojojin Rundunar Operation Fansan Yamma suka gano harsasai 1,207 hannunsu.
Kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom ya ce an kama su ne a hanyars ta kai wa ’yan ta’addan da ke addabar yankin Arewa maso Yamma makaman.
Ya ce matar mai shekaru 18 mijin masi shekaru 40 suna tsare suna amsa tambayoyi, yana mai jinjina wa sojoji da ’yan banga bisa kwarewar da suka nuna wajen kama miyagun.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link