’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta samu nasarar ceto wasu mutum uku da aka sace, bayan wani samame da ta kai a jihohin Kano da Kaduna.
Wannan na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi domin yaƙi da laifuka da tabbatar da tsaron jama’a.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne tsakanin ranar 7 zuwa 9 ga watan Oktoba, 2025, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori.
A cewar Kiyawa, samamen farko ya gudana ne a ranar 7 ga watan Oktoba.
Ya ce runduna ta musamman ta yaƙi da garkuwa da mutane tare da haɗin gwiwar tawagar sintiri ta sashen ’yan sanda na Bebeji suka kai samame, bayan samun bayanan sirri.
An ceto mutanen ne, bayan wani matashi mai shekaru 21, mai suna AbdulHamid Bello, wanda aka sace, ya yi nasarar tserewa daga hannun masu garkuwa da shi, ya sanar da ’yan sanda inda aka ajiye shi.
Wannan ya taimaka wajen gani maɓoyar masu garkuwar da ke ƙauyen Saya-Saya, a Ƙaramar Hukumar Ikara ta jihar Kaduna, inda suka samu nasarar ceto wani mutum mai suna Musa Idris, mai shekaru 65.
Masu garkuwar sun tsere bayan ganin ’yan sanda, inda suka bar babur da igiya.
Daga baya, an mayar da waɗanda aka ceto zuwa ga iyalansu tare da kai su asibiti don kula da su.
A wani lamari daban da ya faru a ranar 9 ga watan Oktoba, ’yan sanda sun kuma ceto wani matashi mai shekaru 19 mai suna Ashiru Murtala, wanda aka sace a ranar 5 ga watan Oktoba a ƙauyen Beli da ke Ƙaramar Hukumar Rogo ta Jihar Kano.
Masu garkuwar sun bar shi a gonar rake da ke Hunkuyi,a Jihar Kaduna, inda ’yan sanda suka same shi cikin ƙoshin lafiya.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, ya umurci a kula da lafiyar waɗanda aka ceto, tare da tabbatar da cewa rundunar tana ci gaba da neman waɗanda suka tsere.
“Babu wajen ɓoyewa ga masu laifi a Jihar Kano,” in ji CP Bakori, inda ya yaba wa jarumtaka da ƙwazon jami’an da suka kai samamen.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link