Tinubu ya fi damuwa da siyasa sama da rayukan ’yan Najeriya

[ad_1]



Jam’iyyar ADC ta zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin mayar da hankali kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar nan.

Jam’iyyar ta ce shugaban yaf i damuwa 2ajen halartar tarukan siyasa da biki, maimakon kare rayukan ’yan Najeriya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce maganar da Shugaba Tinubu ya yi a Cocin COCIN a Jos, na batun haɗa kan ‘yan Najeriya, ba komai ba ne illa siyasa kawai.

Jam’iyyar ta ce tun da ya hau mulki, ba a ga wani mataki da ke nuna yana son haɗa kan al’umma ba.

ADC, ta ce Najeriya tana fuskantar mummunar barazana daga ’yan bindiga, don haka ta buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin wanzar da zaman lafiya.

“ADC na cikin damuwa sosai saboda yadda Shugaba Tinubu ke nuna rashin damuwa da yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a ƙasar nan,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta soki sugaban saboda ci gaba da halartar bukukuwa da tarukan siyasa, alhali ana kashe mutane da yin garkuwa da su a sassan ƙasar.

ADC ta kafa misali da yadda ’yan bindiga suka addabi ƙananan hukumomi tara a Jihar Kwara, inda mahara ke tilasta wa mazauna yankunan bayar da abinci, abin sha, da kuɗi a matsayin fansa.

Jam’iyyar ta ce wannan babban gazawa ce ta gwamnati, kuma har yanzu fadar shugaban ƙasa ba ta ɗauki mataki ba.

Har ila yau, ta sake kafa misali da Jihar Kogi, inda ’yan bindiga suka kashe fasinjoji tare da sace mata da yara.

Ta ƙara da cewa sama da makarantu 180 a Arewacin Najeriya aka rufe saboda rashin tsaro, lamarin da ya tilasta wa gomman yara zaman gida.

Jam’iyyar ta ce irin waɗannan abubuwa suna faruwa kusan a dukkanin sassan ƙasar nan; daga Filato zuwa Zamfara, Benuwe zuwa Neja, Kaduna zuwa Kwara, inda ake yawan kashe mutane da yin garkuwa da su.

Duk da haka, Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da cewa tana samun “ci gaba.”

ADC ta ce wannan magana ba ta dace ba saboda ana ci gaba da zubar da jinin al’umma.

Sanarwar ta ƙara da cewa yayin da al’umma a karkara ke tserewa daga gidajensu, ake rufe makarantu, Shugaba Tinubu yana halartar bukukuwa da jana’izar ’yan siyasa.

A cewar ADC, wannan yana nuna cewa ya fi damuwa da harkokin siyasa sama da rayukan ’yan ƙasa.

Haka kuma, ta soki yadda Tinubu yake zama a fadar gwamnati yana aike saƙon ta’aziyya bayan kisan jama’a, maimakon ɗaukar mataki tun kafin irin waɗannan hare-hare su auku.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *