Fitaccen ɗan jarida a Kano, Aliyu Abubakar Getso ya rasu




Allah Ya yi wa fitaccen ɗan jarida a Jihar Kano Aliyu Abubakar Getso, rasuwa da safiyar yau Lahadi bayan fama da rashin lafiya.

Abubakar Getso ya yi aiki a kafafen yaɗa labarai da dama da suka haɗar da na gwamnati da kuma masu zaman kansu.

Ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya da jikoki da dama.

Iyalai sun ce za a yi jana’izarsa da misalin karfe 9:30 na safiyar yau Lahadi a gidansa da ke Second Gate a Unguwar Janbulo, Kabuga.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *