Gwamna Namadi ya raba wa mata 1,400 tallafin kayan ɗinkin hula a Jigawa

[ad_1]



Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ƙaddamar da shirin tallafa wa mata 1,400 da kayan sana’ar ɗinkin hula domin bunƙasa harkokin kasuwancinsu.

A wajen bikin raba kayan, Gwamna Namadi ya ce ɗinkin hula tsohuwar sana’a ce da mata suka gad tun daga iyaye da kakanni, wadda ke taimaka musu wajen dogaro da kai da kuma kula da iyalansu.

Waɗanda suka ci gajiyar wannan shiri na farko, sun fito daga ƙananan hukumomi bakwai na masarautar Dutse, waɗanda suka haɗa da Dutse, Kyawa, Birnin Kudu, Buji, Gwaram, Jahun da Miga.

Gwamnan ya ce da kayan aikin da aka ba su, mace za ta iya ninka yawan hulunan da ta ke ɗinkawa cikin ƙanƙanin lokaci, wanda hakan zai ƙara mata samun kuɗaɗe da zaman lafiya a cikin gida.

Ya ƙara da cewa wannan shiri matakin farko ne na manufar gwamnatinsa na bunƙasa sana’o’in gargajiya zuwa masana’antu masu inganci nan gaba, inda ƙananan sana’o’i za su iya girma su koma manyan masana’antu.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin, a madadin ragowar matan, Hajara Sani, ta ce wannan tallafi zai taimaka musu sosai.

“Muna gode wa Gwamnan kan wannan tallafi. Tabbas za mu yi amfani da kayan yadda ya ce saboda kowa a nan yana murna. Kuma za mu bai wa mara ɗa kunya da yardar Allah,” in ji ta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *