An shiga taron gaggawa kan takun saƙar PENGASSAN da Matatar Dangote
Shugabannin ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) da wakilan Matatar Dangote na halartar wani taron gaggawa tare da wakilan Gwamnatin Tarayya.
Shugaban ƙungiyar PENGASSAN, Festus Osifo, tare da Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (TUC), Nuhu Toro, ne ke jagorantar ɓangaren ƙungiyoyin ƙwadago, yayin da Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Maigari Dingyadi da wasu jami’ai ke wakiltar Gwamnatin Tarayya.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamnatin Tarayya ta gayyaci shugabannin PENGASSAN da na ɓangaren Matatar Dangote zuwa wannan taro sakamakon rikicin da ke tsakanin ɓangarorin biyu.
Sai dai, duk da cewa an tsara fara taron da misalin ƙarfe 2:00 na ranara Litinin, an soma shi da misalin ƙarfe 3:50 na yamma saboda jinkirin isowar wasu manyan masu ruwa da tsaki, kafin daga bisani a shiga bayan labule.
Da yake jawabi a taron, Minista Dingyadi ya ce: “Abin da ke faruwa yau yana da matuƙar muhimmanci ga tattalin arziƙin ƙasa da tsaron ƙasa baki ɗaya, la’akari da cewa PENGASSAN ta shiga yajin aiki.”
Babu shakka a yayin da rikici yake ƙara sama a tsakanin ma’aikata da Matatar Dangote, PENGASSAN ta tsunduma wani yajin aikin da ya tsaida ayyuka a kusan duk harkar mai na Nijeriya.
Duk da ƙoƙari na tsomin baki a bangaren mahukuntan Najeriya dai daga duk alamu an yi tsaiwa irin ta gwamen jaki a tsakanin ’yan ƙungiyar PENGASSAN da ke cewa Matatar Dangote ba ta da ikon korar wasu ma’aikata sama da 800 bisa ’yancinsu na shiga ƙungiyar
Tun da sanyin safiyar yau dai ne ma’aikata suka rufe ofisoshi da hukumomi da ke kula da harkar man, wani abu da ke kama da kokari na aike sako.
Ma’aikatan dai sun rufe ofisoshin hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya (NMDPRA) da hukumar makamashi ta Najeriya (ECN), da kuma hukumar kula da haƙo man fetur ta NUPRC.
A halin yanzu, masana’antu da hukumomin mai na fuskantar matsin lamba saboda rufe wuraren aiki, yayin da jama’a ke bayyana damuwa kan yiwuwar tasirin wannan rikici ga farashin mai da samun man fetur a ƙasar.