An kama buhun tabar wiwi 150 bayan hatsarin mota a Kano
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama buhu 150 maƙare da tabar wiwi a yayin da ake tsaka aikin ceto bayan wani hastarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kano.
Hukumar ta bayyana cewa hatsarin ya auku ne tsakanin wata mota ƙirar Volkswagen Golf da wata babbar mota a yankin Gadar Tamburawa da ke Jihar Kano.
Kakakin NDLEA na Jihar Kano, ASN Sadiq Mohammed Maigatari, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin fasinjojin da aka ceto ya yi ƙoƙarin tserewa amma an yi nasarar kama shi.
Ya ce a yayin bincike ne aka gano buhuna 150 na tabar wiwin wanda nauyinsu ya kai kilogram 112.
Ya ƙara da cewa direban motar ya shaida musu cewa shi ne ya yiwo dakon tabar wiwin madadin mai ita, kuma ba wannan ne karon farko ba da ya yi safarar ta zuwa Kano da wasu wurare.
Direban ya bayyana cewa ya yi aron hannu ne domin kauce wa shingen binciken jami’an NDLEA, a garin haka aka samu hatsarin na ranar Asabar.
Ya ƙara da cewa direban babbar motar ya samu karaya, sauran mutum biyu da aka kama suke tsare.