SEMA ta raba kayan tallafi ga gidaje 90 a Gombe

[ad_1]



Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta raba kayan tallafi ga al’ummar Jalingo-Kamo da ambaliyar ruwa ta shafa a Karamar Hukumar Kaltungo, inda iftila”in ya shafi gidaje kimanin 90.

Rabon kayan ya biyo bayan umarnin Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda ya amince da bayar da kayan abinci da na masarufi domin rage raɗaɗin da jama’ar da abin ya shafa suke ciki.

Yayin rabon kayan a fadar Hakimin Jalingo-Kamo, Sakataren Hukumar SEMA, Alhaji Abdullahi Haruna Abdullahi ya ce sun gudanar da cikakken bincike da ƙirga waɗanda abin ya shafa kafin rabon.

Abdullahi ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici tare da isar da saƙon ta’aziyyar Gwamnan ga al’ummar da iftila’in ta rutsa da su.

Ya jaddada cewa, tallafin an bayar da shi ne don rage wahala ba wai a matsayin diyya ba.

A nasa jawabin, Jagoran Majalisar Dokokin Jihar Gombe kuma Ɗan Majalisa mai wakiltar Kaltungo ta Gabas, Yerima Ladan Gaule ya yi ta’aziyya ga waɗanda abin ya shafa tare da tabbatar musu da ƙudirin gwamnati na ci gaba da kula da al’umma a kowanne hali.

Ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da mara wa gwamnatin Inuwa Yahaya baya domin ci gaban jihar.

Da yake mayar da jawabi Hakimin Jalingo-Kamo, Alhaji Abdullahi Musa a madadin waɗanda iftila’in ya shafa  ya gode wa Gwamna Inuwa Yahaya, da Ɗan majalisar da Hukumar SEMA bisa wannan taimako.

Sai dai ya roƙi gwamnati da ta gina hanyoyin mota domin bunƙasa ci gaban yankin tare da samar da fitilun titi don inganta tsaro.

Kayan da aka raba sun haɗa da: Buhunan shinkafa da taliya da tabarma da zannuwa da tufafin yara da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *