An harbe ’yan sanda 3 har lahira a Kogi
[ad_1]
Wasu mahara sun harbe jami’an ’yan sanda uku har lahira da safiyar ranar Laraba a wata madakatar mota da ke garin Egbe, a Ƙaramar Hukumar Yagba Yamma a Jihar Kogi.
Kakakin rundunar jihar, SP William Aya, ne ya tabbatar da harin.
Ya ce harin ya faru ne a kan iyakar Jihar Kogi da Jihar Kwara.
SP Aya, ya ƙara da cewa, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Miller Dantawaye, ya tura tawaga ta musamman domin bincika yankin domin kama waɗanda suka kai harin.
“Ina tabbatar muku cewa ’yan sandanmu uku sun mutu a Egbe yau.
“Kwamishina ya tura tawaga ta musamman, kuma muna bibiyar waɗanda suka kai harin. Za a kama su duka,” in ji Aya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link