Cin amana shi ne tsarin siyasa a Najeriya — Jonathan
[ad_1]
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce siyasar Nijeriya ta ginu ne a kan cin amana, la’akari da irin cin amanar da ya ce ya fuskanta matuƙa a lokacin da yake neman tazarce a Zaben 2015.
Jonathan ya bayyana haka ne a wurin bikin cika shekara 70 na tsohon abokinsa, Cif Mike Aiyegbeni Oghiadomhe, da aka gudanar a Benin, babban birnin Jihar Edo, a ranar Alhamis.
Ya ce daga cikin abubuwan da ya fahimta a siyasar Najeriya shi ne wahalar samun ɗan siyasa mai gaskiya da tsayawa a kan kalamansa.
A cewarsa, galibin ’yan siyasar Nijeriya ba su da riƙon gaskiya ko amana, sai dai ya yaba da Oghiadomhe a matsayin mutumin da ya fita daban cikin ’yan siyasar ƙasar.
“A halin yanzu siyasar Nijeriya ta ta’allaƙa ne da cin amana. Saboda zai yi wuya ka samu ɗan siyasar da zai faɗi wani abu ɗaya da safe, ya tsaya a kai har zuwa rana ko zuwa yamma.
“A cikin ’yan mintuna kaɗan za su faɗi abu ɗaya, amma bayan awa guda sai su sauya magana,” in ji Jonathan.
Sai dai ya bayyana cewa Cif Oghiadomhe na daga cikin ’yan siyasa ƙalilan da zai iya sadaukar da rayuwarsa saboda shi.
“A wurina, Oghiadomhe mutum ne da za a iya kai kalamansa banki a ajiye, saboda gaskiyarsa da amana. Amma yawancin ’yan siyasa kuwa, ba za ka iya dogaro da kalamansu ba,” in ji shi.
Ana iya tuna cewa, Cif Oghiadomhe ne ya yi wa Jonthan Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa daga 2010 zuwa 2014, wanda tsohon shugaban ya nanata jin daɗin alaƙarsa da shi.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai tsohon shugaban APC na ƙasa, Sanata Adams Oshiomhole, tsofaffin gwamnonin Edo, Lucky Igbinedion da Oserheimen Osunbor, tsohon Gwamnan Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo, tsohon Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnatin Edo, Farfesa Izia Ize-Iyamu da sauran jiga-jigai.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link