Saudiyya ta ƙaƙaba wa masu laifukan rashin ɗa’a sabuwar tara
Gwamnatin Saudiyya ta sanar da sanya tarar kuɗi kan masu aikata ayyukan da suka shafi rashin ɗa’a a cikin al’umma, musamman a lokutan salla, domin kare mutunci, tsaro da kuma zaman lafiya.
Sabbin matakan, wanda za a fara aiwatarwa nan take, sun shafi masu sanya kaya marasa mutunci a bainar jama’a, da masu kunna kiɗa lokacin salla, da masu bahaya ko zubar da shara a wuraren da doka ta haramta.
A cewar sabuwar doka, duk wanda aka kama da kunna kiɗa a lokacin salla zai biya tara ta Riyal 1,000 (kimanin Naira 390,000) a karon farko, kuma idan aka sake kama shi, tarar za ta ninka zuwa Riyal 2,000 (kimanin Naira 780,000).
Haka kuma, duk wanda ya sa tufafi marasa mutunci a bainar jama’a za a ci shi tara ta Riyal 100, sannan idan ya sake maimaitawa tarar za ta ƙaru zuwa Riyal 500.
An kuma haramta zubar da shara ko bahaya a wuraren da doka ta hana. Kuma duk wanda ya karya wannan doka a karon farko zai biya Riyal 500, sannan a karo na biyu tarar za ta ninka zuwa Riyal 1,000.
Bugu da ƙari, duk wanda aka kama yana ɗaukar hoto ko bidiyo ba tare da izini ba, za a ci shi tara ta Riyal 1,000, sannan idan ya maimaita laifin tarar za ta ninka zuwa Riyal 2,000.
Sabbin dokokin na Saudiyya na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke ƙoƙarin ƙara tsaurara matakan ladabtar da jama’a, musamman a wuraren ibada da jama’ar musulmi ke taruwa.