Duk budurwar da ta ci kuɗin saurayi kuma ta ƙi zuwa wajensa ta karya doka – ’Yan sanda
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta yi gargadin cewa sabon salon da ’yan mata suka fito da shi na karbar kudin samarinsu da nufin za su je wajensu amma su ki zuwa laifi ne da za a iya hukunta su da shi.
A cikin wani bidiyo da Kakakin rundunar a jihar, Grace Iringe-Koko, ta wallafa ranar Laraba, ta ce yin hakan daidai yake da da damfara, kuma za a iya hukunta duk wacce ta aikata.
A cewar kakakin, “Me ya sa za ki karbi kudi daga wajen mutum kuma ki ki zuwa wajensa, hakan laifi ne da mai aikata shi zai iya fuskantar hukunci.
“Yin hakan hukuncinsu daya da mallakar kudade ta hanyar yaudara wanda ake kira da 419,” in ji Grace.
Kakakin ta kuma ce yin hakan daidai yake da aikata laifin zamba cikin aminci wanda idan wanda aka yi wa laifin ya kai kara za a iya hukunta wacce ta aikata.
Daga nan sai ta yi kira ga sauran jama’a da su guji damfarar mutane ta hanyar saba alkawari.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link