2027: ’Yan adawa na ƙoƙarin sanya APC fara kamfe da wuri — Tinubu
[ad_1]
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya zargi jam’iyyun adawa da jan APC cikin harkokin siyasa kafin lokacin zaɓen 2027.
Sai dai ya ce ba zai bari hakan ya karkatar da hankalinsa daga shugabantar Najeriya ba.
Yayin da yake ganawa da gwamnonin Arewa maso Gabas a Abuja, Tinubu ya yaba da ƙoƙrinsu wajen yaƙi da rashin tsaro tare da alƙawarin yin aiki da su kan batun ’yan sandan jihohi da kuma ayyukan gina hanyoyi.
“A siyasa, ’yan adawa suna ƙoƙarin janyo mu mu fara kamfen da wuri. Amma duk da haka, ba zan bari a karkatar da hankalina ba. Na mayar da hankali ne kan abin da ke gabana,” in ji Tinubu.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, wanda ya yi magana a madadin sauran gwamnonin, ya tabbatar wa shugaban ƙasa da goyon bayansu.
Ya bayyana matsalolin tsaro a Arewa maso Gabas tare da roƙon ƙarin tallafin Gwamnatin Tarayya.
“Muna goyon bayan shirin shugaban ƙasa na horas da ma’aikata da kuma samar da fasaha domin rage matsalar ta’addanci da inganta harkar noma,” in ji Zulum.
Gwamnonin sun kuma roƙi shugaban ƙasa ya kammala manyan hanyoyi, ya ci gaba da aikin haƙo mai a Kolmani da Tafkin Chadi, da kuma ci gaba da ayyukan soji a yankin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link