Tinubu ya dawo da shugaban NTA da aka sauke
[ad_1]
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da tsohon Shugaban Gidan Talbijin na Nijeriya, NTA da aka sauke kwanan nan, Salihu Abdullahi Dembos.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a watan Oktoban 2023, a yanzu zai dawo domin kammala wa’adin mulkinsa na shekara uku.
Haka ma shugaban ƙasar ya bayar da umarnin maido da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA, domin shi ma ya ƙarasa wa’adinsa na shekara uku da zai ƙare a 2027.
A ’yan kwanakin nan ne aka sanar da sauke Dembos sakamakon wasu sauye-sauye da aka gudanar da hukumar.
Sauke shi dai ya janyo zazzafar muharawa da suka musamman daga yankin arewacin ƙasar, inda Salihu Abdullahi Dembos ya fito.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link