Gwamnan Neja ya rushe kwamishinoninsa
[ad_1]
Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya rushe majalisar kwamishinoninsa.
Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce gwamnan ya sanar da rushe majalisar kwamishinoninsa ne a yayin taron Majalisar Zartarwa ta jihar a safiyar Litinin ɗin nan.
Ya kuma yaba musu bisa gudunmawar da suka bayar wajen kawo ci-gaba mai ma’ana a jihar tare da yi musu fatan alheri.
Sai dai kuma gwamnan ya sake nada sakataren gwamnatin da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da mataimakinsa a da wasu jami’ai a kan muƙamansu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link