Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 12, sun ƙwato makamai a Borno
[ad_1]
Dakarun Operation Haɗin Kai (OPHK) tare da Civilian JTF, sun yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 12 a Jihar Borno.
A ranar 29 zuwa 30 ga watan Agusta, sojojin sun kai farmaki ƙauyukan Tamsu Ngamdu, Dalakaleri, Gaza da Loskori Kura, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan.
A Loskori Kura, sojojin sun yi nasara, inda suka kashe ’yan ta’adda 12, suka kuma kwato8 bindiga ƙirar AK-47 guda shida, harsasai guda takwas da magunguna iri-iri.
Majiyoyin tsaro sun ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun ji raunuka, bayan artabun da suka yi da sojojin.
Wannan farmaki ya lalata hanyoyin sadarwar ’yan ta’addan da dabarunsu a yankin, ya kuma haifar musu da cikas.
Wannan nasara na zuwa ne a dai-dai lokacin da dakarun Nijeriya ke ƙara kai hare-hare ta ƙasa da sama a Arewa maso Gabas, musamman a dajin Sambisa, tafkin Chadi da tsaunin Mandara, domin kawo ƙarshen ta’addanci.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link