’Yan bindigar da suka sace ma’aurata a Katsina na neman N600m




’Yan bindigar da suka sace wani mutum, matarsa da ’yarsu a Jihar Katsina, na neman Naira miliyan 600 a matsayin kuɗin fansa.

Wanda aka sace sun haɗa da Anas Ahmadu mai shekara 33, matarsa Halimat, da kuma ’yarsu Jidda.

An sace su ne a gidajensu da ke Filin Canada Quarters a Sabuwar Unguwa, cikin garin Katsina da safiyar ranar Talata.

A yayin kai harin, wani ɗan sa-kai mai shekara 25 mai suna Abdullahi Muhammad, ya rasu lokacin da yake ƙoƙarin ceto su.

Wani ɗan uwan ma’auratan ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kira ɗan uwan Halimat, Malam Ibrahim, ta wayar Anas domin neman kudin fansa Naira Miliyan 600.

Sai dai iyalan sun bayyana cewa ba za su iya biyan wannan kuɗi ba.

Radda ya dawo daga hutu saboda hare-haren ’yan bindiga a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya dawo daga hutun jinyar da yake yi a ƙasashen waje, sakamakon sabbin hare-haren ’yan bindiga a jihar.

A ranar Laraba, gwamnan ya kai ziyara ta’aziyya ƙauyen Gidan Mantau, a Karamar Hukumar Malumfashi, inda ’yan bindiga suka kashe masallata a wani masallaci a ranar 19 ga watan Agusta.

Shaidu sun ce harin ya auku ne a lokacin da jama’a ke yin sallar Asuba.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai harin ne a matsayin ramuwar gayya, bayan da mutanen yankin suka yi musu kwanton-ɓauna, tare da kashe mutanensu sannan suka ƙwace musu makamai da babura.

Hakazalika, an ruwaito cewa ’yan bindigar sun ƙone sama da mutum 20 a gidajensu lokacin da suka sake kai hari Gidan Adamu Mantau, a Unguwar Yar Mai Dabo, Makera da kuma Burdigau.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *