Ba zan tsaya takarar kowanne irin mukami ba a 2027 – El-Rufai




Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba zai tsaya takarar kowanne irin mukami ba a zaben 2027, inda ya ce burinsa kawai ya samar wa jiharsa da Najeriya nagartattun shugabanni.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Kaduna, lokacin da ya karbi wasu matasa karkashin jagorancin Aliyu Bello da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC.

El-Rufa’i ya kuma soki lamirin gwamnati mai ci, inda ya ce ’yan Najeriya na ganin gazawarta karara ba tare da wani ya musu karin bayani ba.

“Ba abin da wannan gwamnatin ke yi ban da karya a kullu-yaumin. Kowa ya san gaskiya. Ni ba na neman kowacce irin kujera. Ba zan tsaya takarar Sanata ba ko ma kowanne irin matsayi, shi ya sa nake rokonku da ku zo mu hada hannu mu kori azzalumai,” in ji shi.

Ya ce a baya abin da ya tsara shi ne bayan ya sauka daga Gwamna zai yi ritaya daga harkokin siyasa gaba daya, amma abubuwan da ke faruwa ne suka tailasta masa dawowa, kodayake babu bukatar kashin kansa a ciki.

Tsohon Gwamnan ya ce burinsa shi ne ya taimaki matasa da mata da masu rajin kawo ci gaba domin su karbe ragamar siyasa su kawo canjin da ake bukata.

Daga nan sai ya bukaci mutane da su je su yi rajistar zaben da aka fara domin shiga harkokin zabe ka’in da na’in.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *