ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe

[ad_1]



Shirin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL) ya raba wa ƙungiyoyin manoma 47 a Jihar Gombe, buhunan iri na zamani 6,220 don bunƙasa harkar noma.

An gudanar da rabon ne yayin taron kwanaki biyar na masu ruwa da tsaki kan kula da manyan koguna na Gongola, Gali-Lamurde da Hawal-Kilunga, wanda yake ɗaya daga cikin muhimman ayyukan ACReSAL a Najeriya.

Shugaban shirin a Jihar Gombe, Dokta Sani Adamu Jauro, ya ce Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna jajircewa wajen tallafa wa manoma ta hanyar shirin.

Ya ƙara da cewa an samu nasarori kamar shuka bishiyoyi a dukkanin ƙananan hukumomi 11, rage zaizayar ƙasa da kuma kare muhalli.

Kwamishinan Noma da Kiwo na jihar, Barnabas Malle, wanda Ibrahim Sajo ya wakilta, ya yaba wa shirin tare da shawartar manoma da su yi amfani da irin wajen noma.

Ya ce gwamnati ta riga ta fara sayar da taki mai rangwame don sauƙaƙa wa manoma.

Shugaban Kungiyar Manoma (AFAN) a Jihar, Alhaji Ahmed Modibbo Nafada, ya bayyana tallafin a matsayin babban taimako musamman ga shirin noman rani.

Ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnati wajen rage rikicin manoma da makiyaya a jihar.

A nata ɓangaren, Sakatariyar Ƙungiyar Mata Manoma (SWOFON) reshen Gombe, Hannatu Iliya Yila, ta ce mambobinsu sama da 5,000 za su amfana da shirin.

Ta kuma roƙi gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙara tallafa wa mata manoma da taki da magungunan kashe ƙwari.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *