HOTUNA: Yadda JNI ta yi jana’izar mambobinta da aka kashe a harin Jos
[ad_1]
Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ta binne mambobinta huɗu da aka kashe a harin da aka kai a Anguwan Rukuba da ke Jos, a Jihar Filato.
Harin ya faru ne a daren ranar Lahadi a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.
Aƙalla mutum 28 aka tabbatar sun rasu, yayin da wasu da dama suka jikkata.
A ranar Asabar, wasu daga cikin ’yan uwan waɗanda abin ya shafa sun taru tare da Babban Limamin Masallacin Juma’a na Jos, Sheikh Ghazali Ismaila Adam, domin gudanar da jana’izar mamatan.
An gudanar da jana’izar a cikin maƙabartar Babale, domin kauce wa tashin hankali a cikin al’umma.
Babban Limamin, wanda ya jagoranci sallar, ya jajanta wa iyalan mamatan, tare da roƙonsu da su yi haƙuri su kuma ɗauki lamarin a matsayin ƙaddara daga Allah.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su guji yin kalaman da ka iya ƙara tayar da hankali, yana mai jaddada cewa babu abin da ya fi zaman lafiya.
Ga hotunan yadda aka gudanar da jana’izar:
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link