Kungiyar Manoman Citta Ta Kasa Ta Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Kan Tallafin Da Take Ba Su
[ad_1]
Shugaban kungiyar masu noman citta na kasa, Nuhu Bagani Daudu, ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin tarayya kan ci gaba da tallawa manoman Citta da kara masu kwarin guiwa da take yi.
Nuhu a hirarsa da manema labarai a Jihar Kaduna, ya kuma jinjina wa gwamnatin tarayya da gwamnatin Jihar Kaduna, kan kara bunkasa nomanta a jihar.
- Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan PDP A Kaduna, Ashiru, Zai Koma ADC A Ranar Lahadi
- CBN Ya Ɗage Tsarin Dijital, Zai Biya Mahajjata Kuɗin Guzurinsu A Hannu
Ya kuma yaba wa gwamnatin, kan bayar da umarnin fitar da kudi, musamamn domin kara wa manoman kwarin guiwar rungumar yin noma na zamani.
Sai dai, ya kuma yi kira ga gwamnatin da ta tallafa wa manoman da sauran kayan aiki, musamaman taki da magungunan kashe kwari da ingantaccen irin noma da kuma sauran kayayyakin nomanta.
Ya kuma yi kira ga manoman na Citta, da su rungumi yin noma da kayan aiki na zamani, musmman domin su kara habaka sana’ar su.
Nuhu ya kuma nuna jin dadinsa, kan yadda a kwanan baya ake dakile barkewar cutar da ke lalata cittar da aka shuka a Jihar Kaduna.
Shugaban ya kara da cewa, kungiyar na kuma yin aiki kafada da kafada da masu hada-hadar sayar da citta da masu sarrafa ta, tare da kuma fitar da ita zuwa ketare, domin kara samun gwaggwabar riba.
[ad_2]
Source link