Sin Za Ta Sanya Fa’idojin Tattara Bayanai Su Amfanar Da Jama’ar Duk Duniya

[ad_1]

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kafuwar kungiyar tattara bayanai ta duniya ta nuna cikakkiyar amincewar al’ummar duniya game da matakin bunkasar tattara bayanai a kasar Sin. Kuma, Sin za ta kiyaye ka’idoji na tattaunawa tare, da yin ayyuka tare, da kuma cin moriya tare don tallafa wa kungiyar tattara bayanai ta duniya wajen taka muhimmiyar rawa, da kuma tabbatar ganin fa’idojin bayanai sun amfanar da jama’ar duk kasashen duniya.

Mao Ning ta bayyana haka ne a gun taron manema labarai na yau da kullum da aka gudanar yau Jumma’a. Dangane da kalaman da ba su dace ba da Amurka ta yi kan batun tashoshin jiragen ruwa a Panama, Mao Ning ta ce, kalaman Amurka ba su da tushe, kuma suna karkatar da gaskiyar lamarin. Kalamai marasa dacewa da Amurka ta yi sau da yawa suna fallasa yunkurinta a kan mashigin ruwa na Panama.

Bugu da kari, game da harin saman da sojojin Amurka suka kai wanda ya lalata gadar amfanin fararen hula a Iran kuwa, Mao Ning ta bayyana cewa matakin soja da Amurka da Isra’ila suka dauka kan Iran ba tare da izini daga MDD ba, ya saba wa dokokin kasa da kasa. Sin tana adawa da hare-hare kan kayayyakin fararen hula, kuma ya kamata bangarorin da abin ya shafa su tsagaita bude wuta nan take, su koma kan hanyar diflomasiyya wajen magance matsalolin ta fuskar siyasa.(Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *