Kwankwaso ya haɗe da Atiku da Obi don yaƙar Tinubu a 2027
[ad_1]
A yau ne ake sa ran madugun tafiyar Kwankwasiyya kuma Jagoran Jam’iyyar NNPP na Ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai sauya sheƙa zuwa Jami’yyar adawa ADC a hukumance.
A ƙarshen mako ya sanar da ficewarsa daga NNPP, a daidai lokacin da ’yan adawa ke shirye-shiryen da neman tsara lissafin siyasarsu domin ƙwace mulki daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC, wanda ke neman wa’adi na biyu a babban zaɓen shekarar 2027.
Komawar Kwankwaso, wanda shi ne tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, zuwa sabuwar Jam’iyyar ADC, zai ba shi damar haɗewa da tsofaffin abokan takararsa a zaɓen 2023— tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da kuma Peter Obi na Jam’iyyar Labour—domin haɗa ƙarfi a ƙarƙashin inuwa da nufin kayar da Tinubu a zaɓen 2027.
Dawowar Kwankwaso ADC, wadda bisa dukkan alamu ita ce jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a halin yanzu, na zuwa ne bayan ya yi watsi da tayin da Jam’i yyar APC ta yi masa na dawowa cikinta.
Tasirin komawar Kwankwaso ADC
Ana sa ran shigar Kwankwaso ADC tare da dubban magoya bayansa, musamman ’yan Kwankwasiyya zai ƙara wa Jam’iyyar ƙarfi da farin jini, musamman ganin yadda a zaɓen 2023 ya kai Jam’iyyar NNPP ga ƙwace kujerar Gwamnan Jihar Kano da sana’o’i biyu da mafi yawan kujerun Majalisar Wakilai da Majalisar Dokoki ta Jihar Kano daga hannun jam’iyya mai mulki.
Tuni dai wasu gaggan ’yan siyasa da muƙarraban Gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari, suka koma Jam’iyyar ADC, wacce tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata David Mark, yake jagoranta, bayan sun raba gari da Gwamnatin Tinubu.
Daga cikinsu akwai tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida kuma tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai da tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami da sauransu, waɗanda yanzu suke zaman doya da manja da APC da Gwamnatin Tinubu.
Masu sharhi na ganin rashin irin wannan haɗin gwiwar ce ta ba wa Tinubu nasara a kan Atiku da Kwankwaso da Obi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ya ba wa kowannensu tazara mai yawa, duk kuwa da miliyoyin ƙuri’un da kowannensu ya samu.
A zaɓen 2023, Tinubu ya yi nasara da ƙuri’u 8,794,726 a yayin da Atiku na PDP ke biye da shi da ƙuriu 6,984,520, sai Peter Obi na Jam’iyyar LP mai 6,101,533 yayin da Kwankwaso ya samu 1,496,687 a ƙarƙashin inuwar.
Masu hasashe na ganin da manyan ’yan takarar sun haɗe a jam’iyya guda a lokacin, da tuni sun kayar da Tinubu.
Zuwa yanzu dai babu tabbacin cewa irin wannan lissafin ne ya haɗa waɗannan manyan tsofaffin ’yan takarar shugaban ƙasa a ADC.
A gefe guda kuma tun bayan lashe zaɓen 2023 zuwa yanzu Jam’iyyar APC mai mulki ta yi nasarar zawarto kusan dukkan zaɓaɓun shugabannin siyasa daga jam’iyyun adawa, inda a halin yanzu take da kusan 32 daga cikin 36 da ke ƙasar nan, baya ga samun rinjaye a Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai da majalisun dokoki na jihohi. Baya ga tsofaffin gwamnoni da sauran manyan ’yan siyasa da suka koma APC.
Sai dai kuma, komawar Kwankwaso ADC bayan ya yi watsi da APC da tayin da ta yi masa, ya nuna jam’iyya mai mulki tana da jan aiki a Kano, jihar da ta fi kowacce yawan ƙuri’u a Najeriya, duk da komawar Gwamna Abba Kabir Yusuf cikinta daga NNPP.
APC ta yi ta ƙoƙarin tattaunawa domin janyo Kwankwaso zuwa cikinta, amma majiyoyi sun ce ɓangarorin ba su daidaita ba a kan sharuɗɗan da ya gindaya wa jam’iyyar.
Ana cikin haka ne Gwamna Abba da magoya bayansa suka kasa kiransa, inda suka yi gaba suka bar shi.
- Ƙuri’un Kano bayan shigar Kwankwaso ADC
Komawar Gwamna Abba Kabir Yusuf APC ta haifar da ruɗani a cikinta a Kano, musamman sauyin shugabanci da rabon muƙamai da kuma daidaita buƙatu, tsakanin tsofaffin ’yan jam’iyya waɗanda suka biyo Abba, wanda tsohon uban gidansa na siyasa, Kwankwaso ya taka rawar gani wajen samun nasararsa a zaɓensa a 2023.
Dawowar Abba APC ta kuma sauya lissafin jam’iyyar, lamarin da ya tilasta Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, jingine aniyarsa ta neman fitowa takarar gwamna a zaɓen 2027.
A ɓangaren Gwamna Abba kuma, akwai ƙalubale, musamman kan yiwuwar samun nasarar wa’adinsa na biyu, da kuma kawo wa Shugaba Tinubu ƙuri’un jihar a zaɓen 2027 ba tare da Kwankwaso ba.
A ɓangaren Kwankwaso kuma, kamar Abba, yana buƙatar sake ƙarfafa yawan magoya bayansa masu amana.
Sauyin sheƙar tasa kuma, ta nuna alamun gazawar jam’iyyar NNPP wajen kai shi ga hadafinsa, da kuma amfanin faɗaɗa haɗin gwiwa domin kaiwa ga nasara.
A yayin da aka ganin komawarsa a matsayin ƙarin ƙarfi ga ɓangaren ’yan adawa, hakan kuma zai ƙara fitowa muhimmancin Kano a matsayin jiha mai mafi yawan ƙuri’u a yayin da jam’iyya mai mulki da ’yan adawa ke shirin kai bantensu a zaɓen 2027.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link