Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar NNPP

[ad_1]



Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Kwankwaso, ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bayan yin nazari kan yanayin siyasar Najeriya a halin yanzu.

“Ganin yadda yanayin siyasar ƙasar yake tafiya a halin yanzu, wanda ke buƙatar sake yin nazari, na ga ya zama dole na koma wani dandali da zai ba ni damar kawo sauyi a faɗin ƙasar nan.”

Ya bayyana cewa burinsa shi ne kasancewa a sahun jam’iyyar da za ta ba shi damar kawo sauyi na gaske a faɗin ƙasar.

Ya ƙara da cewa lokacin da ya shafe a NNPP abin alfahari ne a gare shi, sai dai ya ce yanke shawarar barin jam’iyyar ba abu ne mai sauƙi ba.

“A matsayina na mamba mai kishin jam’iyyar, yanke wannan shawarar barin jam’iyyar ba abu ne mai sauƙi ba,” in ji shi.

Kwankwaso ya bayyana cewa sauye-sauyen siyasa ne suka sanya ya ga dacewar komawa sabuwar jam’iyya.

Hakazalika, ya miƙa godiyarsa ga shugabannin jam’iyyar, musamman Shugabanta na Ƙasa, Ajuji Ahmed, da sauran mambobi bisa goyon bayan da suka ba shi.

Ya kuma gode wa ɗaukacin magoya bayan ƙungiyar Kwankwasiyya da sauran shugabanni a dukkanin matakai.

“Za mu ci gaba da haɗa kai da yin aiki tare domin gina makoma mai kyau da samar wa ƙasarmu ci gaba”.

Daga ƙarshe, Kwankwaso ya tabbatar da cewa duk da ficewarsa daga NNPP, zai ci gaba da aiki ƙafa-da-ƙafa da sauran masu kishin ƙasa domin ci gaban Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *