Bankin Duniya ya Jinjina Wa Jihar Gombe Kan Magance Zaizayar Kasa

[ad_1]

Wata tawaga daga Bankin Duniya, karkashin jagorancin Daraktan Bankin a Nijeriya, Matthew Berghis, ta nuna jin dadinta ga girma, inganci da tasirin ayyukan daure kwari da magance zaizayar kasa da ake gudanarwa a Jihar Gombe.

Tawagar, tare da rakiyar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ta kai ziyarar gani da ido wurin Aikin Daure Kwari da Zaizayar Kasa na FCE (Technical), inda suka duba aikin mai tsawon kilomita 21 da aka aiwatar a karkashin shirin ACReSAL.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Zamfara
  • Saraki Ya Soki Gwamnatin Kwara Kan Ƙaruwar Rashin Tsaro

A wurin aikin, wakilin kamfanin Triacta Nigeria Limited, Injiniya Imran Khan, ya bada cikakken bayanin yadda aikin ya gudana, yana mai bayyana cewa aikin ya hada da gine-ginen kankare da aka karfafa da dabarun inganta yanayi wadda aka tsara don farfado da kasar da ta zaizaye don dakile wata sabuwar zaizayar.

Ya jaddada cewa tsarin na aikin hadin gwiwa yana karfafa juriya da inganta muhalli na dogon lokaci.

Shi ma da yake jawabi, Ko’odinetan shirin ACReSAL na jiha, Sani Adamu Jauro, ya bayyana tasirin aikin wajen inganta rayuwar al’ummar yankin.

Ya ce aikin ya wuce na samar da ababen more rayuwa kawai, ya ma hada da tallafin inganta rayuwa ga al’ummomin da abin ya shafa, inda fiye da masu cin gajiyar shirin 100 ke amfana da wuraren sarrafa shara da cibiyoyin tattara ruwan sama.

Ya kara da cewa an bude wani asusun taimakekeniya na al’umma wanda yake da fiye da Naira miliyan 350 don karfafa harkokin tattalin arzikin mazauna yankin.

Wasu masu cin gajiyar shirin da suka yi jawabi a lokacin ziyarar sun bada shaida mai gamsarwa, suna masu yabawa wannan mataki da ya farfado musu da bege, da inganta rayuwa da kuma kare gidaje da gonakansu daga mummunar illar zaizayar ƙasa.

A wani mataki na nuna kara karfafa kudurin alkinta muhalli, Daraktan Bankin na Duniya da Jakadan Tunisiya a Nijeriya, Mohsen Antit, sun yi dashen bishiyoyi don tallafawa ƙudurin Gwamna Inuwa Yahaya na mayar da Gombe koriya shar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *