Dandalin Boao Na Shekara-shekara Na 2026 Ya Gudanar Da Muhimmin Zama A Hainan
A yau Alhamis ne aka gudanar da zaman taro na shekara-shekara na dandalin tattaunawa na nahiyar Asiya na Boao, wato BFA a takaice, na shekarar 2026 a Boao da ke lardin Hainan na kudancin kasar Sin
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’a ta kasar Sin, Zhao Leji ya halarci taron tare da gabatar da muhimmin jawabi.
Yayin da yake nuni da cewa, wannan shekara ce ta cika shekaru 25 da kafuwar dandalin BFA, Zhao ya bayyana cewa dandalin ya zama wani fage mai daraja na karfafa mu’amala, hadin gwiwa, da ci gaba na bai-daya tsakanin kasashen Asiya da ma sauran duniya.
Ya ce, ta hanyar yin aiki tare cikin hadin kai ne kurum dan’adam zai iya magance matsaloli da dimbin kalubalen duniya, tare da gina kyakkyawar makomar rayuwa.
Wanda aka kafa a shekarar 2001, dandalin BFA kungiya ce ta kasa da kasa mai zaman kanta, kuma ba ta neman riba ba, wadda ke jajircewa wajen inganta hadewar tattalin arzikin yanki da kuma kusantar da kasashen Asiya ga cimma burikansu na ci gabansu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)