’Yan Najeriya kada su zaɓi ADC, ba ta da abun bayarwa — Shettima
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya shawarci ‘yan Najeriya kada su goyi bayan jam’iyyar ADC, inda ya ce babu wani abu da za ta iya bayarwa.
Ya yi wannan magana ne a ranar Laraba a filin baje koli na Gusau da ke Jihar Zamfara, yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyarsa.
Shettima ya ce ADC “ba komai ba ce,” inda ya kwatanta ta da ƙashin da ba shi da nama ko kaɗan.
“Shin kun san ADC? Ba ta da abin da za ta ba ku, don haka kada ku bi ta,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar ba ta da abin da da ake buƙata domin jagorantar ƙasa ko kawo ci gaba ga ’yan Najeriya.
Wannan kalamai nasa sun jawo hankalin jama’a a yayin da ake ci gaba da tunkarar babban zaɓen 2027.