Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Tarwatsa Gada A Neja Domin Daƙile Harin Sojoji

[ad_1]

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a ranar Litinin sun tayar da bam a wata gada da ke kan titin Luma a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja, da nufin katse ayyukan sojoji a yayin da ake ci gaba da yaƙi da ta’addanci.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na dare. Majiyoyi sun ce gadar da lamarin ya shafa tana haɗa al’ummomin Luma, Babana da Agwara, waɗanda suka sha fama da hare-hare a ‘yan kwanakin nan.

Mazauna yankin sun kuma bayyana cewa, tarwatsa gadar ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci a babbar kasuwar iyaka ta Babana, wacce take gudana duk ranar Litinin.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce maharan, waɗanda ake kyautata zaton suna ɓoye ne a gandun dajin Kainji, sun yi amfani da wani abun fashewa ne wajen lalata gadar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *