Abincin Sallah

[ad_1]

Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.

A yau shafin na mu zai koya mana Fried Rice da Kaza da Zobo domin yin abincin Sallah:

A lokutan bukukuwa kamar Sallah ko taron biki, mutane da yawa suna son shirya abinci mai da di da kuma abin sha mai sanyaya rai. Daga cikin abincin da ake yawan yi akwai Fried Rice da Nama ko Kaza da Zobo ku kunun Aya ko na zaki.

Kayan hadin fried rice:

Shinkafa, Karas, Wake koraye (green beans), Albasa, Mai, Gishiri, Kayan yaji kamar Kuri da tiyim, da maggi.

Yadda ake hadawa:

Da farko a wanke shinkafa a tafasa ta kadan da gishiri. Bayan haka a soya Albasa a cikin Mai, sai a zuba karas da wake koraye a juya. A zuba kori, Tiyim da Maggi, sannan a zuba shinkafar da aka tafasa a gaureya sosai har ta dadu.

Yadda ake yin kaza:

A wanke kaza a zuba Gishiri, Maggi, Kori, Tiyim da Albasa. A tafasa ta kadan, sannan a dora Mai a soya ta har ta soyu.

Yadda ake yin zobo:

A wanke ganyen zobo sosai sannan a tafasa shi da ruwa da citta da kanunfari da bawon Abarba tana kara kamshi, amma ba dole bane idan ba bu na ‘yan mintuna. Bayan haka a tace ruwan, a zuba sukari da dan Abarba ko Lemun Tsami domin kara dandano idan ana so za a iya sa Cola ko ire-iren su. A sa shi a firiji domin ya yi sanyi kafin a sha.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *