2027: Ba Ni Da Tabbacin Samun Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa A ADC — Peter Obi

[ad_1]

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya bayyana cewa bai da tabbacin samun tikitin tsayawa takara na jam’iyyar ADC gabanin zaɓen shekarar 2027.

A wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, Obi ya ce duk da goyon bayan da yake samu, ba zai iya cewa tabbas jam’iyyar za ta ba shi tikitin takara ba.

  • Nijar Ta Haramta Fitar Da Dabbobi Ketare Don Takaita Karancinsu A Cikin Gida
  • ADC Ta Gargadi APC Kan Tilasta Wa Ma’aikatan Gwamnati Yin Rijistar Jam’iyyar

Ya ce abin da ya fi muhimmanci a gare shi shi ne manufar da suke fafutuka a kai, ba wai burin kansa na siyasa kaɗai ba.

Obi ya kuma nuna damuwa kan yadda al’amuran siyasa suka rikiɗe, yana mai cewa yana yawan tunanin yadda aka kai ga wannan matsayi da kuma abin da zai faru idan suka daina wannan ƙoƙari.

Ya gode wa magoya bayansa bisa juriya da sadaukarwarsu, yana mai cewa ba abu ne mai sauƙi ba kasancewa a ɓangaren adawa a Nijeriya ba, tare da jaddada cewa zai ci gaba da tsayawa kan manufofinsa duk da ƙalubalen da ke akwai.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *