Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutun ƙaramar sallah
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis da Juma’a, wato 19 da kuma 20 ga watan Maris a matsayin ranakun hutun ƙaramar Sallah a Najeriya.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka a wata sanarwa da babbar Sakatariyar ma’aikatarsa, Dokta Magdalene Ajani ta fitar a ranar Talata.
Sanarwar tana kuma yi wa Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan da zagayowar bikin ƙaramar sallah ta Eid-el-Fitr.
Ya yi kira ga Musulmi da su kwaikwayi halayen Manzon Allah S.A.W da suka ƙunshin kyautatawa, nuna soyayya, haƙuri, juriya da kuma zaman lafiya.
Kazalika, ya yi kira ga ɗaukacin ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin bukukuwan domin yi wa ƙasar addu’ar samun ci gaba da zaman lafiya, haɗin kai, da wadata.
Ministan ya ƙarfafa gwiwar ’yan kasa da su yi murna mai ma’ana cikin nutsuwa tare da sadar da ayyukan alheri ga mabuƙata a cikin al’umma.
Ya ba da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya ta duƙufa wajen samar da haɗin kan ƙasa da zaman lafiya a tsakanin ‘yan Nijeriya baki ɗaya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link