Mazauna Yankin Sun Tsere Bayan Gano Wasiƙar Kawo Hare-haren Ta’addanci a FCT

[ad_1]

Mazauna da dama na al’ummomin Kungaboku da Paze a cikin Babban Birnin Tarayya (FCT) sun tsere daga gidajensu bayan wata wasiƙa da ake zargin ‘yan bindiga ne suka rubuta ta bayyana, wadda ke barazanar kai hare-hare a yankin.

A cikin wasiƙar da aka ce an samu a cikin littafin wani ɗalibi a wata makaranta mai zaman kanta, ‘yan bindigar sun yi rantsuwa cewa za su kai hari Kungaboku da makwabciyarta Paze domin ramuwar gayya kan kashe kwamandansu.

  • Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Birnin Paris
  • Ƙarin Farashin Fetur: Ƙungiyar Ƙwadago Ta Nemi A Dakatar Da Karɓar Haraji

Za a iya tuna cewa a ranar 7 ga Maris, sojojin Bataliya ta 7, tare da ‘yansanda da ‘yan sa-kai, sun ceto mutane 19 da aka sace.

Wadanda aka ceto, mafi yawansu mazauna Paze da Kungaboku ne, sun samu ‘yanci ne yayin wani hadin gwiwar bincike da aikin ceto da aka gudanar a yankin Gidan Dogo da ke Karamar Hukumar Bwari.

A yayin wannan aiki, an ruwaito cewa sojojin sun kashe wani ɗan bindiga, yayin da sauran suka tsere daga wurin da raunukan harbin bindiga da ake zargin sun samu.

An kuma ruwaito cewa an gano wasiƙar barazanar ne a cikin littafin rubutun wani ɗalibi a wata makaranta mai zaman kanta da ke Paze, bayan da wani malami ya gano ta yayin da yake duba aikin gida na ɗalibin.

Bayan sanarwa mahukunta makarantar, ‘yansanda sun kama ɗalibin, iyayensa, malamin da kuma shugabannin makarantar domin yi musu tambayoyi da bincike, kafin daga bisani aka sake su.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa Kungaboku da Paze, wadanda ke kusa da Byazhin, dake cikin Kubwa a Karamar Hukumar Bwari, sun sha fama da hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan kwanakin nan.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *