NPA Ta Samu Ƙaruwar Kashi 24.8 Na Kayayyakin Da Ke Shigowa Daga Ƙasashen Waje
[ad_1]
Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya, (NPA), ta sanar da samun ƙaruwar jimillar kayan da aka sarrafa da kashi 24.8 cikin 100 a shekarar 2025, lamarin da ta bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan lokutan ci gaba a tarihin harkokin sufurin ruwa na ƙasar.
A cewar Rahoton Ayyukan Hukumar na 2025, jimillar kayan da aka sarrafa ta ƙaru daga kimanin tan miliyan 103.6 a shekarar 2024 zuwa sama da tan miliyan 129.3 a shekarar 2025.
- Abin Da Ya Sa Hukumar SON Ta Ƙarfafa Haɗaka Da Hukumar NPA
- Sanatocin Da Ba Su Kawo Ƙudiri Ba Tun Bayan Ƙaddamar Da Majalisar Dattawa Ta 10
Rahoton ya nuna cewa Lekki Deep Sea Port ita ce tashar jiragen ruwa mafi girma a Nijeriya, inda ta ɗauki kashi 40.6 cikin 100 na dukkan kayan da aka sarrafa a ƙasar. Onne Port ta biyo baya da kashi 19.1 cikin 100, yayin da Apapa Port ta sarrafa kashi 16.7 cikin 100.
Baya ga yawan kaya, Tashar Lekki ta kuma karɓi manyan jiragen ruwa mafiya girma, inda ta yi rajistar matsakaicin (GRT) na 55,712, wanda ya ɗan fi na Onne Port mai 53,022 GRT.
Tashar Apapa da tashar Tin Can Island sun yi rajistar matsakaicin girman jiragen ruwa na GRT 33,251 da 36,909 bi da bi, yayin da Tashar Delta ta karɓi jiragen ruwa masu matsakaicin GRT 17,414.
Duk da cewa Tashar Tin Can Island ce ta fi yawan zuwan jiragen ruwa, inda ta kai kashi 22.7 cikin 100 na dukkan kiraye-kirayen jiragen ruwa, tashoshin Lekki Deep Sea Port da Tashar Onne na ci gaba da jawo manyan jiragen ruwa masu nauyi, lamarin da ke ƙara ƙarfin Nijeriya wajen sarrafa kayayyaki masu daraja mai yawa.
Shigo da kaya ya fi yawa, amma fitar da kaya na ƙara samun gindin zama
Duk da cewa shigo da kaya ya ci gaba da rinjayar zirga-zirgar kayayyaki, rahoton ya nuna ƙaruwar da ake samu a fitar da kaya zuwa waje a hankali. Fitar da kaya ta kai kashi 39.0 cikin 100 na jimillar kayan da aka sarrafa, yayin da shigo da kaya ya kai kashi 59.2 cikin 100.
Masana harkokin kasuwanci sun bayyana ƙaruwar yawan kayayyakin da ake fitarwa a matsayin tabbaci na ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tattalin arziki domin rage dogaro da ɗanyen mai da kuma ƙarfafa fitar da kayayyakin da ba na mai ba.
Kayayyakin da ake jigilar su a cikin kwantena, wanda ake ɗauka a matsayin muhimmin ma’aunin auna harkokin kasuwanci, sun samu gagarumar ƙaruwa. Jimillar zirga-zirgar kwantena ta ƙaru da kashi 25.7 cikin 100, inda ta haura miliyan 2.1 na ma’aunin Twenty-foot Eƙuiɓalent Units (TEUs).
Kwantena masu ɗauke da kayayyakin shigo da kaya sun ƙaru da kashi 32.8 cikin 100, yayin da na fitar da kaya suka ƙaru da kashi 3.1 cikin 100. Abin lura shi ne, kwantenan da ake sauya musu hanya sun samu ƙaruwar kashi 205.8 cikin 100, lamarin da ke nuna cewa Nijeriya na tasowa a matsayin cibiyar hada-hadar sufuri da kayayyaki a yankin Yammaci da Tsakiyar Afirka.
Kayayyakin ruwa masu yawa (liƙuid bulk cargo), ciki har da kayayyakin man fetur da sinadarai, sun ci gaba da kasancewa mafiya rinjaye, inda suka kai kashi 54.7 cikin 100 na jimillar kayayyakin da aka sarrafa, yayin da kayayyakin da ake jigilar su a cikin kwantena suka kai kashi 24 cikin 100.
Da yake tsokaci kan rahoton, Manajan Darakta na Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa na Nijeriya (NPA), Dakta Abubakar Dantsoho, ya bayyana nasarorin shekarar 2025 a matsayin wani muhimmin tarihi.
Ya ce, “Ɓangaren sufurin ruwa na Nijeriya ya samu gagarumin ci gaba a shekarar 2025, sakamakon ƙaruwar yawan kayayyakin da aka sarrafa, ƙarin zirga-zirgar kwantena da kuma faɗaɗar fitar da kaya zuwa waje. Wannan na nuna ƙudurin Gwamnatin Tarayya na bunƙasa tattalin arziki ta hanyar rage dogaro da ɓangare guda.”
Masana sun kuma lura cewa ƙaruwar girma da nagartar jiragen ruwa da ke sauka a tashoshin jiragen ruwan Nijeriya na nuna yadda ake daidaita ayyukan da ƙa’idojin sufurin ruwa na duniya, lamarin da ke ƙara wa ƙasar gasa a kasuwannin yankuna da na ƙasa da ƙasa.
Da yake duban gaba, Dantsoho ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa shirin sabunta tashoshin jiragen ruwa da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi, tare da aiwatar da tsarin National Single Window, za su ƙara ingiza sabon matakin ci gaba a ɓangaren.
Wannan cikakken shirin sabunta tashoshin jiragen ruwa na da nufin gyara tsofaffin kayayyakin more rayuwa, zurfafa wuraren da jiragen ruwa ke sauka (berths), inganta dandalin sauke kaya (ƙuays), faɗaɗa ƙarfin sarrafa kayayyaki da kuma amfani da sabbin hanyoyin fasahar zamani a dukkan tashoshin jiragen ruwan Nijeriya.
Ana sa ran sauye-sauyen za su rage lokacin da jiragen ruwa ke ɗauka kafin su kammala ayyukansu, su taƙaita tsawon lokacin da kaya ke zama a tashar, su kara inganta matakan tsaro da kuma bunƙasa ingancin gudanar da ayyuka baki ɗaya.
Yayin da ci gaban da fitar da kaya ke jagoranta ke ƙara samun karɓuwa, kuma yawan kayayyakin da ake sauya musu hanya ke ƙaruwa sosai, Rahoton Ayyukan 2025 na nuna wani gagarumin sauyi a ɓangaren sufurin ruwa na Nijeriya. Wannan na sanya Lekki Deep Sea Port da sauran tashoshin jiragen ruwa na ƙasar a tsakiyar ƙoƙarin faɗaɗa tattalin arziki da kuma burin kasuwancin yankuna na Nijeriya.
[ad_2]
Source link