Rashin Shugabanni Masu Cikakken Shiri Ne Matsalar Afrika – Obasanjo
[ad_1]
Tsohon shugaban ƙasar, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa rashin ingantaccen shugabanci ne babban abin da ke hana ci gaban ƙasashen Afrika.
Obasanjo ya faɗi haka ne a ranar Alhamis a birnin Abeokuta yayin da yake jawabi ga waɗanda suka kammala karatu a Olusegun Obasanjo Leadership Institute, a wani taro da aka gudanar a lokacin bikin laccar ranar haihuwarsa ta 89 mai taken “The Global Africa Enlightenment: From Chains to Renaissance.”
- GDPn Nijeriya Ya Yi Ƙasa Fiye da Na Shekaru 20 da Suka Wuce A Zamanin Obasanjo — Hashim
- Rikicin Boko Haram Ya Daɗe Fiye da Yaƙin Basasar Najeriya – Obasanjo
Taron ya samu halartar manyan mutane da suka haɗa da Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, tare da gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun da wasu tsoffin gwamnonin jihar.
Obasanjo ya ce bayan sama da shekaru 50 da ya shafe yana hidimar jama’a, ya fahimci cewa babbar giɓin da Afirka ke da shi ba kuɗi ba ne ko ƙasa ko ilimi, illa shugabanci.
Ya ƙara da cewa shugaba mai hangen nesa, da gaskiya, da jajircewa wajen yi wa al’umma hidima na iya sauya al’umma, ceto cibiyoyi, tare da mayar da ƙasa kan turbar ci gaba.
[ad_2]
Source link