Gwamna Lawal Ya Haramta Karbar Kuɗaɗen Shiga Da Tsabar Kuɗi A Zamfara
[ad_1]
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi a faɗin jihar, domin ƙarfafa tsarin fasahar zamani, haɗa bayanan hukumomi wuri guda, bai wa gwamnati damar sa ido kai tsaye, da kuma rage asarar kuɗaɗen shiga ta hanyar toshe duk wata kafa ta bayan fage.
Gwamnan ya bayyana wannan umarni ne a ranar Juma’ar da ta gabata yayin taron tattaunawa da wayar da kai kan Dokokin Gyaran Haraji na Nijeriya 2025, wanda Hukumar Tara Harajin Cikin Gida ta Jihar Zamfara ta shirya a Gusau, babban birnin jihar.
- Matatar Dangote Ta Ƙara Farashin Fetur, Ta Dakatar Da Lodi
- Kotu Ta Ƙi Amincewa Da Bukatar Tsoffin Kwamishinonin Kano Na Riƙe Motocin Gwamnati
A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, taron mai taken “Bunƙasa Hanyoyin Samun Kuɗaɗen Shiga a Sabon Tsarin Haraji: Binciko Damar Kuɗaɗen Shiga Da Ba Na Haraji Ba A Zamfara” ya tattaro dukkan masu ruwa da tsaki daga sassan jihar.
Manufar taron ita ce samar da fahimta mai zurfi da haɗin kai yayin da jihar ke shirin aiwatar da sabon tsarin haraji.
A jawabinsa, Gwamna Lawal ya bayyana cewa Dokokin Gyaran Haraji na 2025 sun sake fasalin tsarin haraji a ƙasa baki ɗaya, inda aka fayyace iyakoki, aka daidaita hanyoyin aiki, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin matakan gwamnati uku.
Ya ce, rattaba hannu kan dokar sake fasalin Dokar Haɗaɗɗen Asusun Kuɗaɗen Shiga na Jihar Zamfara, wato Zamfara State Consolidated Revenue Law ya ƙara bai wa hukumar karbar kuɗaɗen shiga ta jihar ƙarfin ikon tantancewa, karba da kuma lissafa dukkan kuɗaɗen shiga na jihar, tare da daidaita kuɗaɗen haraji da waɗanda ba na haraji ba a ƙarƙashin tsari guda.
A cewarsa, gyare-gyaren sun zo da dama da kuma nauyi. Damar ita ce gina tsarin kuɗaɗen shiga na zamani, mai inganci da ke kare masu biyan haraji tare da ƙarfafa kwarin gwiwar masu zuba jari. Nauyin kuwa shi ne dukkan hukumomin gwamnati su daidaita aikinsu da sabon tsarin doka da gudanarwa.
Gwamnan ya jaddada cewa tara kuɗaɗen shiga ba aikin hukuma guda ba ne, illa wajibi ne na dukkan ma’aikatu, sassa da hukumomi. Duk wata hukuma da ke karbar kuɗi ta hanyar kuɗaɗe, lasisi, izini ko hidima dole ta tabbatar da gaskiya, daidaito da miƙa kuɗaɗe cikin gaggawa ta hanyoyin da aka amince da su.
Ya gargaɗi cewa duk wata hanya ta boye-boye, maimaituwa ko karbar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba za a ɗauki mataki a kai. Ya bayyana aniyar gwamnatinsa na rufe dukkan gibin da ke haddasa asarar kuɗaɗen shiga domin tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka tara suna komawa wajen ci gaban jama’a.
Gwamna Lawal ya bayyana cewa alƙaluman IGR na 2025 sun nuna an samu ci gaba, amma har yanzu akwai buƙatar ƙara ƙarfafa tsarin tattara kuɗaɗen shiga. Ya ce burin jihar na tara tsakanin Naira biliyan 38 zuwa 42 ya ginu ne kan ajandar gyaran da aka fara da kuma faɗaɗa tsarin bin ƙa’ida.
A yayin taron, an karrama wasu ma’aikatu, hukumomi da ɗaiɗaikun mutane bisa jagoranci da ƙwazo wajen miƙa kuɗaɗen shiga ga gwamnati yadda ya kamata.
[ad_2]
Source link