Jakadan Amurka na shan caccaka kan halasta wa Isra’ila mamaye Gabas ta Tsakiya

[ad_1]

Ƙasashen Larabawa da na Musulmi sun yi Allah-wadai da kalaman jakadan Amurka a Isra’ila, Mike Huckabee, wanda ya nuna cewa Isra’ila na da “haƙƙi a addinance” na mallakar yanki mai faɗin gaske a Gabas ta Tsakiya.

Huckabee, wanda tsohon fasto ne na Cocin Baptist kuma mashahurin mai goyon bayan Isra’ila, ya faɗi hakan ne a wata hira da ya yi a shirin Tucker Carlson.

A shirin da aka fitar a ranar Juma’a, Carlson ya tambayi Huckabee kan ma’anar wata ayar Littafi Mai Tsarki da wasu ke fassara a matsayin cewa Isra’ila na da ‘yanci kan ƙasar da ta shimfiɗa daga kogin Nilu a Masar zuwa kogin Euphrates a Siriya da Iraƙi.

A martaninsa, Huckabee ya ce: “Ba matsala ba ne idan sun karɓi dukkan yankin.”

Sai dai daga baya ya ɗan lashe amansa, yana mai cewa Isra’ila “ba ta nemi karɓar dukkan wannan ba,” tare da cewa maganarsa “ta wuce gona da iri ce kawai.”

Haka kuma, a ranar Asabar, Huckabee ya wallafa wasu saƙonni biyu a shafin X yana ƙara fayyace wasu batutuwa da aka taɓo a hirar, amma bai sake magana kan batun ayar Littafi Mai Tsarki ba.

Fushi kan wannan kalami na jakadan ya ƙaru ne a ranar Lahadi, inda fiye da ƙasashe goma sha huɗu na Larabawa da Musulmi tare da manyan ƙungiyoyi uku na yankin, suka fitar da sanarwar haɗin gwiwa suna siffanta kalaman jakadan Amurkan a matsayin “masu haɗari da kuma tayar da hankali.”

Sanarwar, wadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta fitar a ranar Lahadi, na ɗauke da sa hannun ƙasashen UAE, Masar, Jordan, Indonesia, Pakistan, Turkiyya, Saudiyya, Qatar, Kuwait, Oman, Bahrain, Lebanon, Siriya da Falasɗinu.

Haka kuma, Kungiyar Haɗin Kai ta Musulunci ta Duniya da Majalisar Larabawan da ta yankin Gulf wato Arab League da Gulf Cooperation Council sun sanya hannu.

Sun ce kalaman sun saɓa wa Kundin Tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya kuma suna kawo cikas a ƙoƙarin da ake yi wajen yayyafa wa wutar yaƙin Gaza ruwan sanyi da kuma samar da mafita ta siyasa mai ɗorewa.

Ƙasar Iran ma ta shiga sahun masu suka, inda ma’aikatar harkokin wajenta ta zargi Huckabee a shafin X da tana mai cewa “haɗin kai kai-tsaye na Amurka” a abin da ta kira “yaƙe-yaƙen faɗaɗa ƙasa” da Isra’ila ke yi kan Falasɗinawa.

Sukar da ƙasashen Larabawa suka yi

Tun da farko, wasu ƙasashen Larabawa sun riga sun fitar da nasu kalaman sukar daban-daban.

Saudiyya ta bayyana kalaman jakadan a matsayin “sakaci” da “rashin ɗa’a,” yayin da Jordan ta ce hakan “hari ne kan ikon ƙasashen yankin.”

Kuwait ta ce kalaman “cin mutuncin ƙa’idodin dokar ƙasa da ƙasa” ne, yayin da Oman ta ce sun “barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali” a yankin.

Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta jaddada cewa “Isra’ila ba ta da ikon mallakar ƙasashen Falasɗinu da aka mamaye ko wata ƙasar Larabawa.”

Hukumar Falasɗinu (PA) a shafin X cewa ta yi kalaman Huckabee “sun saɓa wa matsayar Shugaban Amurka Donald Trump na ƙin amincewa da mamayar Yammacin Kogin Jordan.”

Isra’ila ta yaba wa Huckabee

A gefe guda, Shugaban Majalisar Dokokin Isra’ila, Amir Ohana, ya yaba wa Huckabee a shafin X kan goyon bayan Isra’ila da ya nuna a hirar, tare da zargin Carlson da “yaɗa ƙarya da ruɗani.”

A kwanakin baya-bayan nan, Carlson ya fuskanci zarge-zargen nuna ƙiyayya ga Yahudawa, musamman bayan wata doguwar hira da ya yi da Nick Fuentes—wanda ya bayyana kansa a matsayin mai ra’ayin fifikon fararen fata, ya yaba wa Hitler, ya musanta Holocaust, kuma ya zargi Yahudawan Amurka da rashin aminci.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *