‘Yansanda Sun Yi Alƙawarin Bayar Da Cikakken Tsaro A Kano
[ad_1]
Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yansanda, AIG, wanda ke kula da hedikwatar rundunar, shiyya ta 1, da ke Kano, Ahmed Garba, ya sake tabbatar da kudurin rundunar ‘yansandan Nijeriya na kare rayuka da dukiyoyi.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar shiyyar, CSP Bashir Mohammed ya fitar a Kano ranar Talata.
Garba ya yi wannan bayanin ne yayin da ya kira taron bitar dabarun aiki da Kwamandoji da masu Leken asiri na rundunar ‘yansanda daga jihohin Kano da Jigawa.
Kwamandojin sun tattauna hanyoyin ƙarfafa ayyukan tsaro da ake gudanarwa kuma sun amince da matakan tura ƙarin jami’ai daga rundunar ‘yansanda tare da haɗin gwiwar rundunar soji zuwa al’ummomin da ayyukan ‘yan ta’adda ke shafa a shiyyar.
AIG Garba ya roƙi mazauna shiyyar da su ba da haɗin kai ga hukumomin tsaro ta hanyar samar da ingantattun bayanai don tallafawa ƙoƙarin da ake yi na dakile ayyukan ‘yan fashi da makami da sauran manyan laifuka.
[ad_2]
Source link