Tsagin PDP Mai Biyayya Ga Wike Ya Sanya 23 ga Mayu, Domin Zaɓen Fidda Gwani Na Shugaban Ƙasa
[ad_1]
Wani ɓangare na jam’iyyar PDP mai biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya sanya ranar 23 ga Mayu, 2026 domin gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, alamar fara wani muhimmin tsari na cikin gida na zaɓen ɗan takarar jam’iyyar.
An cimma wannan matsaya ne a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) karo na 106 na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, inda shugabannin jam’iyyar suka amince da cikakken jadawalin gudanar da dukkan zaɓukan fidda gwani bisa ƙa’idojin hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Da yake gabatar da sanarwar bayan taron, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na kwamitin riƙo, Jungudo Mohammed, ya bayyana jadawalin da aka amince da shi.
Ya ce: “Kwamitin NEC ya duba batun gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyya a mukamai daban-daban da kuma jadawalin warware takaddamar da ka iya tasowa daga waɗannan zaɓukan.
NEC ta kuma buƙaci dukkan sassan jam’iyyar da masu ruwa da tsaki su fara shirye-shiryen da suka dace tare da bin jadawalin da aka amince da shi da kuma dukkan tanade-tanaden doka.”
Bisa ga jadawalin:
- Jam’iyyar za ta miƙa rajistar mambobinta ga INEC ranar 10 ga Afrilu, 2026.
- Zaɓen fidda gwani na Majalisun Dokokin Jihohi zai gudana 2 ga Mayu.
- Na Majalisar Tarayya, zai kasance 9 ga Mayu.
- Zaɓen fidda gwani na gwamnonin jihohi zai gudana 16 ga Mayu.
- Daga ƙarshe, za a gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa ranar 23 ga Mayu.
[ad_2]
Source link