Tinubu ya faɗa wa ’yan Najeriya dalilin sauya hafsoshin tsaro — ADC

[ad_1]



Jam’iyyar ADC ta nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana wa ’yan Najeriya ainihin dalilin da ya sa ya sauya hafsoshin tsaron ƙasa ba zato ba tsammani.

Aminiya ta ruwaito yadda shugaban ƙasa ya sauya hafsoshin tsaron da ya naɗa shekaru biyu da suka wuce.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya ce jam’iyyar ta damu ganin yadda aka yi sauyin ba zato ba tsammani bayan jita-jitar yunƙurin juyin mulki.

“Ko da yake shugaban ƙasa yana da ikon yin irin waɗannan sauye-sauye, amma mum damu da wannan mataki biyo bayan jita-jitar yunƙurin juyin mulki,” in ji Abdullahi.

Ya ƙara da cewa amsar da gwamnatin ta bayar game da wannan jita-jitar ba yi cikakken bayani ba face ruɗani da ta jefa mutane a ciki.

ADC ta ce irin wannan sauyi na iya haifar da ruɗani a rundunar sojoji, don haka dole ne a samu dalilai masu ƙarfi kafin a yanke irin wannan hukunci.

Jam’iyyar, ta ce gwamnati tana da alhakin bayyana wa ’yan ƙasa ainahin abin da yake faruwa .

“Mu a matsayin jam’iyyar adawa, muna son zaman lafiya da ɗorewar dimokuraɗiyya a ƙasarmu.

“Abin da ke faruwa a maƙwabtan ƙasashe kamar Chadi da wasu ƙasashen yankin Sahel ya ƙara mana damuwa,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da rashin mayar da hankali, inda ta bayyana cewa matsalar tsaro na ƙara ta’azzara yayin da ’yan ta’adda da ’yan fashi ke sake yin ƙarfi a wasu yankuna na ƙasar.

“Sauya hafsoshin tsaro ba zai warware waɗannan matsalolin ba. Maimakon haka, zai sa mutane su yi zargin cewa gwamnati ta fi mayar da hankali kan siyasa da mulki sama da kare rayukan ’yan ƙasa,” in ji Abdullahi.

ADC, ta gargaɗi gwamnati cewa sauya dukkanin hafsoshin tsaro a lokaci guda na iya ƙara janyo jita-jita da hasashe marasa tushe.

Saboda haka, jam’iyyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta fito fili ta bayyana gaskiya, tare da tabbatar wa ’yan Najeriya cewa dimokuraɗiyyar ƙasar ba ta cikin hatsari.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *