Salla: Farashin kayan miya ya faɗi, na kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a Taraba

[ad_1]



Mazauna Jihar Taraba na fuskantar wani sabon yanayi yayin da ake shirin bikin Ƙaramar Salla, inda farashin kayan miya da man ja ya faɗi warwas, amma farashin kayan masarufi kamar shinkafa, wake, da masara ya yi tashin gwauron zabi.

A kasuwar Tashan Lau da ke Jalingo ta nuna cewa farashin kayan miya ya ragu, akasin yadda aka saba gani a lokutan bukukuwa inda farashi kan tashi.

Misali, kwandon tumatir da ake sayarwa a kan Naira 6,500 a baya, yanzu ya koma Naira 4,000.

Farashin barkono ya ragu daga Naira 60,000 zuwa Naira 40,000, yayin da buhun albasa ya sauka daga Naira 64,000 zuwa Naira 45,000.

Wani ɗan kasuwa, Mallam Ibrahim Dan Gombe, ya bayyana cewa saukar farashin ya faru ne sakamakon yawan kayayyakin da aka shigo da su daga maƙwabtan jihohi.

Sai dai yayin da kayan miya suka yi sauƙi, farashin hatsi da sauran kayan abinci ya ƙaru.

Mudun shinkafar gida ya tashi daga Naira 1,600 zuwa Naira 2,200, wake ya tashi daga Naira 1,200 zuwa Naira 2,000, yayin da buhun masara mai nauyin kilo 100 ya tashi daga Naira 18,000 zuwa Naira 27,000.

Haka kuma, tsadar rayuwa na shafar harkar sufuri, inda aka samu ƙarancin fasinjoji a tashar mota ta Jalingo, duk da cewa kuɗin mota bai sauya ba sosai.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *