Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare — Zulum
[ad_1]
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin gaggawa a harkar tsaron sararin samaniya, domin hana ’yan ta’adda na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare.
Zulum, ya faɗi haka ne a ranar Juma’a a garin Mafa, bayan wani hari da Boko Haram suka kai.
Ya ce, “Babban abin da nake son magana a kai shi ne amfani da jirage marasa matuƙa. An shaida min cewa sun yi amfani da su a Dikwa, kuma hakan abu ne mai tayar da hankali.”
Gwamnan ya bayyana cewa yawaitar irin waɗannan jirage a hannun mahara barazana ce ga tsaron ƙasa.
“Dole mu haɗa kai domin magance wannan sabon salo,” in ji shi.
Zulum, ya kuma nemi a ƙara tsaurara tsaro a bakin iyakoki da kuma inganta tsaron sararin samaniya.
A cewarsa: “Wannan abu ne da ya kamata a yi cikin gaggawa, ba tare da ɓata lokaci ba.”
Haka kuma, ya yi kira ga jama’ar jihar da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar kai musu bayanan sirri da za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro.
Ya ƙara da cewa: “Mun samu labari cewa za a kai hari a Mafa, kuma mun sanar da hukumomin da ya kamata su sani. Amma ganin yadda abubuwa suka faru, akwai alamun zagon ƙasa, don haka ya kamata a bincika a kuma yi gyara.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link