An sanya dokar hana fita bayan ɓarkewar zanga-zanga kan zaɓen Tanzania
[ad_1]
An sanya dokar hana zirga-zirgar jama’a a Dar es Salaam, babban birnin Tanzania, bayan da ɗaruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsarin gudanar da zaɓen ƙasar.
Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun riƙa yaga hotunan Shugaba Samia Suluhu Hassan tare da ƙona wani ofishin ’yan sanda, yayin da suke zargin cewa akwai son kai da rashin gaskiya na fifita jam’iyya mai mulki, tare da neman gwamnati ta gyara tsarin zaɓe da kuma ba kowa damar faɗar albarkacin baki.
Zanga-zangar dai ta ɓarke ne yayin da ake tattara sakamako bayan kammala kaɗa ƙuri’a a zaɓen na yau Laraba da manyan ’yan takarar adawa walau suke ɗaure ko kuma aka hana su takara baki ɗaya.
Duk da sojoji da tankokin yaƙi da aka jibge a Dar es Salaam da wasu muhimman wurare, ɗaruruwan matasa sun fita tituna suna rera waƙoƙin cewa “muna buƙatar maido mana da ƙasarmu,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Haka kuma wata ƙungiya da ke sa ido kan harkokin Intanet mai suna NetBlocks ta ce an katse layukan sadarwa a fadin ƙasar.
Rahotanni sun ce mutane ba su fito da yawa ba a rumfunan zabe sabannin zabukan baya.
Ana dai sa ran Shugaba Samia Suluhu Hassan ce za ta lashe zaɓen domin yin tazarce a wa’adin mulki karo na biyu.
Samia Hassan ta hau kan mulki daga matsayin mataimakiyar shugaban ƙasa a shekarar 2021 bayan rasuwar wanda ya gabace ta, John Magufuli.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link