‘Yansanda Sun Kama Amarya Kan Zargin Kashe Mijinta Da Guba A Jigawa
[ad_1]
Rundunar ‘Yansandan Jihar Jigawa, ta sanar da kama wata sabuwar amarya bisa zargin sanya guba a abinci da ta kai ga mutuwar mijinta a ƙauyen Gauza da ke Ƙaramar Hukumar Jahun a jihar.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ya fitar a ranar Asabar.
- Sadio Mane: Daga Ƙwallon Cikin Unguwa Zuwa Zakaran Afirka
- Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Abuja Bayan Ziyarar Guinea Da Switzerland
Rundunar ta ce lamarin ya faru ne a yammacin ranar Juma’a 23 ga Janairun 2026, inda wani sabon ango ya rasu bayan ya ci abincin da ake zargin matarsa ce ta sa masa guba.
Sanarwar ta bayyana cewa binciken farko ya nuna marigayin ya ci abincin rana ne a gida, bayan haka ya kamu da matsananciyar rashin lafiya, wanda aka gaggauta kai shi asibiti domin samun kulawar likita, inda daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa yayin da ake masa jinya.
Rundunar ta ƙara da cewa jami’anta na sashen Jahun sun fara bincike nan take, inda suka kama matar marigayin a matsayin babbar wadda ake zargi, wadda ta amsa laifinta a lokacin da take amsa tambayoyi.
A cewar ‘yansanda, waca ake zargin ta bayyana cewa iyayenta ne suka tilasta mata auren, wanda dalilin ya sa ta aikata ɗanyen aikin,
A yanzu dai Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Jigawa, ya bayar da umarnin a mika lamarin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) da ke Dutse domin zurfafa bincike, kafin daga bisani a gurfanar da wace ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci.
[ad_2]
Source link