Majalisar Dattawan Amurka za ta rage ikon Trump kan sha’anin tsaro

[ad_1]



Majalisar Dattawan Amurka ta soma wani yunƙuri na taƙaita ƙarfin iko da shugaba Donald Trump ke da shi na kai hare-hare da yanke shawarar yaƙi ba tare da cikakkiyar amincewar majalisa ba.

Wannan mataki dai ya biyo bayan farmakin da Trump ya kai Venezuela, har ya kai ga kama shugaban ƙasar Nicolas Maduro da mai ɗakinsa, lamarin da bai yi wa majalisar daɗi ba.

’Yan majalisa daga jam’iyyar adawa ta Democrats, tare da mambobi biyar na jam’iyya mai mulki ta Republican, sun kaɗa ƙuri’ar fara shirin, inda aka samu rinjayen ƙuri’u 52 kan 47 masu adawa da ƙudirin a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Ana sa ran majalisar za ta sake zama a mako mai zuwa domin kaɗa ƙuri’ar ƙarshe kan ko za a amince da ƙudurin ko akasin haka, da nufin daƙile ikon shugaban ƙasa kan harkokin tsaro.

Sai dai Shugaba Trump ya yi kakkausar suka ga ’yan majalisar da suka goyi bayan ƙudurin, yana mai cewa matakin rashin hankali ne kuma abin kunya, musamman ganin yadda wasu daga jam’iyyarsa ta Republican suka haɗa kai da ’yan Democrats.

Trump ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Truth Social, inda ya ce yunƙurin na da nufin rage masa ikon kare Amurka.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *