Sin: Babu Wata Kasa Da Za Ta Nuna Ita Ce ‘Yar Sandan Duniya, Ko Ta Yi Ikirarin Zama Alkalin Kasa Da Kasa

[ad_1]

A yau Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, babu wata kasa da za ta rika aikata abubuwa tana nuna ita ce ‘yar sandan duniya ko kuma ta yi ikirarin zama alkalin kasa da kasa.

Mai magana da yawun ma’aikatar ta yi wannan furucin ne a wani taron manema labarai na yau da kullum yayin da take amsa wata tambaya game da halin da ake ciki a Venezuela.

Ta ce kasar Sin ta dage wajen yekuwar ganin dukkan kasashe suna mutunta ‘yancin sauran al’ummomi na zabar hanyarsu ta ci gaba da kansu, da bin dokokin kasa da kasa da manufofi da ka’idojin kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya, tare da ganin manyan kasashe ne musamman ke jagorantar hakan.

Ta kara da cewa Amurka ta yi watsi da matsayin shugaban Venezuela Nicolas Maduro a matsayin shugaban kasa ta hanyar gurfanar da shi a gaban kotu baro-baro a fili da kuma gudanar da abin da wai aka kira da “shari’a” a kotun cikin gida, wanda hakan ya keta ‘yanci da ikon mallakar kasa na Venezuela da kuma kawo cikas ga dorewar dangantakar kasa da kasa cikin kwanciyar hankali. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *