Zai yi wuya Kwankwaso ya goyi bayan Tinubu a 2027 – Buba Galadima

[ad_1]



Jigo a jam’iyyar NNPP kuma na hannun daman tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Buba Galadima, ya ce zai yi wahala Kwankwason ya goyi bayan Shugaban Kasa Bola Tinubu a zaben 2027 da ke tafe.

Buba, wanda ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Tashoshi a ranar Litinin, ya kuma caccaki gwamnatin Tinubu wacce ya ce da gangan take rura wutar rikicin masarautar Kano ta hanyar goyon bayan Sarkin da Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya sauke.

A bara ne dai Gwamna Abba ya sauke Aminu Ado Bayero daga Sarkin Kano sannan ya dawo da Muhammadu Sanusi II kan karaga, amma har yanzu duka su biyun na ci gaba da da’awar sarautar.

Sai dai Buba Galadima ya kuma kore yiwuwar kowanne irin ƙawance tsakanin NNPP da kuma APC a zaben mai zuwa.

Ya cewarsa, “Magana ta gaskiya ni yanzu ma nake jin wannan. Kwankwaso dan siyasa ne da ke tsayawa da ƙafarsa. Ka tuna ya fafata da APC a Kano kuma ya kai ta ƙasa. Kwankwaso bai taɓa faɗa min cewa yana da niyyar goyon bayan Tinubu ba a 2027.”

Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar suna tattaunawa a tsakaninsu, Buba ya ce da akwai maganar da Kwankwason ya sanar da shi.

Ya ce, “Ba ni na fi kusanci da shi ba, amma a siyasance muna mu’amala sosai. Bai taɓa faɗa min wani abu makamancin hakan ba. Bayan duk abin da APC ta yi mana a Kano?

“An naɗa sarakuna biyu a gari ɗaya? Yanzu akwai Sarkin Gwamnatin Tarayya akwai na jiha. Wa yake da ikon naɗa Sarki sannan ya biya shi albashi?” in ji shi.

Ya kuma yi iƙirarin cewa Gwamnatin Tarayya ta fi son Aminu Ado a matsayin Sarkin shi ya sa ta girke masa motocin ’yan sanda akalla 40 suna gadin gidan da yake.

Buba Galadima ya kuma ce gwamnatin na goyon bayan Sarkin ne saboda ta yi imanin zai taimaka ya sa a zaɓe su a 2027.

Sai dai ya ce, “Babu wani Sarki a Kano da zai iya da wa a zaɓi mutum”.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *